Shugaban Majalisar Kasar Turkiyya Mustafa Sentop ya kyamaci ziyarar da sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya kai a yankin Zirrin Gaza da Yahudawa ke zaune ba bisa ka'aida ba.
Sentop, ya yada a shafinsa ta Twitter da cewa "Agwagwa mai jiran barin gado" na shirin barin sawu marasa inganci.
Inda ya kara da cewa "Wannan ziyara da Pompeo ya kai a yankin da dokar kasa da kasa ta bayyana a matsayin ana zama a haramce, bai kasance mataki ga agwagwa mai shirin barin gado da zai samar da zaman lafiya ba sai dai fitina.