Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya (MDD) Antonio Guterres ya ce a cikin shekaru 20 da suka gabata, miliyoyin mutane sun rasa rayukansu a cikin bala’o’in da sauyin yanayi ya haifar.
Antonia Guterres ya yi magana a "Taron Majalisar Dinkin Duniya na Musamman kan Ruwa da Bala'i" karo na 5 da aka gudanar a Brussels, babban birnin Belgium.
Da yake jawo hankali ga alakar kusan dukkan masifu kamar ambaliyar ruwa, hadari, fari, tsunami da zaizayar kasa da ambaliyar ruwa, Sakatare Janar ya bayyana cewa a kowace shekara bala’o’i na tilasta wa mutane miliyan 26 cikin talauci. Guterres ya kara da cewa,
"A cikin shekaru 20 da suka gabata, yawan bala'o'in da suka shafi yanayi sun kusan ninkawa sau biyu daga shekaru 20 da suka gabata, wadanda suka shafi sama da mutane biliyan 4. Wadannan bala'o'in sun lakume rayukan miliyoyin mutane kuma sun haifar da asarar tattalin arziki sama da Dalar Amurka tiriliyan 2.97."
Da yake bayyana cewa ana hasashen cewa kashi 50 na bukatun agajin jin kai zai kasance ne sanadiyyar bala’oi masu nasaba da yanayi a shekarar 2030, Guterres ya jaddada cewa babbar hanya mafi dacewa ta shawo kan wannan matsalar ita ce takaita dumamar yanayi zuwa digiri 1.5.
Guterres ya ja hankali game da bukatar rage fitar da hayaki da kashi 45 cikin dari nan da shekarar 2030 idan aka kwatanta da na shekarar 2010, da kuma samun nasarar rashin fitar da hayaki a shekarar 2050,
"Amma mun yi nisa da cimma wadannan buri, alkawurran da ake dauka a yanzu ba su isa ba kuma hayakin na ci gaba da karuwa."