Saudiyya ta zuba dala biliyan 100 domin zamanantar da masallatai masu Alfarma

Saudiyya ta zuba dala biliyan 100 domin zamanantar da masallatai masu Alfarma

Al-Ghamdi ya ce an zuba waɗannan maƙudan kuɗi ne domin rage cinkoson jama’a da samar da fasahohin zamani da nufin ƙara adadin jama’ar da ke zuwa aikin hajji da umara a ƙasa mai tsarki a kowacce shekara.

Jakadan na Saudiyya ya yi wannan jawabi ne a lokacin da wasu ƴan Najeriya mutum 20 ke shirin tafiya Ibadar Umara bisa gayyata ta musamman da masarautar ƙasar ƙarƙashin jagorancin Sarki Salman Bin Abdul’aziz Al-Saud ta yi musu.

Masarautar Saudiyya ce ƙarƙashin sarki Salman Bin Abdul’aziz Al-Saud ƙarƙashin wani shirinta na musamman data samar ke ɗaukar nauyin mutane a sassan duniya daban-daban domin zuwa Ibadar Umara kyauta, inda a wannan karo ta ɗauki nauyin ƴan Najeriya 20 domin zuwa ƙasa mai tsarki.

Jakadan na Saudiyya a Najeriya ya buƙaci waɗanda suka samu gayyata ta musamman zuwa ƙasar da su kiyaye da dokoki da ƙa’idojin da hukumomi suka shimfiɗa.

Ambasada Faisal bin Ibrahim Al-Ghamdi  ya ce hukumomin saudiyya suna aiki tuƙuru domin hidimtawa baƙin Allah, kuma za su ci gaba da wannan aiki cikin jin daɗi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)