Syria wadda yaƙin fiye da shekaru 12 ya ɗaiɗaita ta, wannan ne karon farko da Saudiya ke miƙa ƙoƙon barar ganin an sassauta mata takunkumai duk da cewa ta na fama da tarin takunkuman ƙasashen duniya tun shekarar 1979 ƙarƙashin jagorancin Hafiz al-Assad mahaifi ga hamɓararren shugaban wanda ƴan tawaye suka kora a farkon watan Disamban bara.
Yayin taron na jiya Lahadi da ya samu wakilcin jami’an diflomasiyyar ƙasashen EU da kuma na ƙasashen gabas ta tsakiya da kacokan ya mayar da hankali kan yadda za a farfaɗo da Damascus daga mummunan koma bayan da ta faɗa ƙarƙashin Assad, Ministan wajen Saudiya Yarima Faisal bin Farhan ya ce ta hanyar sassautawa Syria takunkuman ne kaɗai, ƙasar za ta dawo hayyacinta.
Masarautar mafi ƙarfin tattalin arziƙi a gabas ta tsakiya, na ƙoƙarin ƙarfafa ƙarfin faɗa ajinta ne a Syria a wani yanayi da tasirin Iran ke dusashewa a wannan ƙasa.
Taron na Riyadh wanda ya ƙunshi wakilcin hatta ƙasashe irin Turkiya da Faransa baya ga haɗakar EU a dunƙule da kuma wakilcin Majalisar ɗinkin duniya na zuwa ne bayan buƙatar hakan daga sabon jagoran Damascus Ahmed al-Sharaa da ya ziyarci tarin ƙasashen Larabawa don neman bayansu wajen samun sassaucin takunkuman.
Ƙasashen yamma ciki har da Amurka da EU sun lafta takunkumai kan gwamnatin Assad lokacin da ya fara murƙushe masu zanga-zanga a 2011 takunkuman da suka zama ƙari kan na shekarar 1979 lokacin da Amurka ta zargi Syrian da ɗaukar nauyin ta’addanci waɗanda aka kara yawansu a 2004.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI