Saudiya na tsaka mai wuya dangane da kulla hulda da kasar Isra'ila

Saudiya na tsaka mai wuya dangane da kulla hulda da kasar Isra'ila

Shugaba Trump na bukatar ganin Saudiyar ta kulla yarjejeniya da Isra'ila kafin batun kafa kasar Falasdinu, yayin da ita kuma Saudiyar ke bukatar ganin kasar Falasdinu kafin mayar da cikakkiyar hulda da Israila.

Yarjejeniyar tsagaita wutar da ta fara aiki yau, kwana guda kafin rantsar da Trump ta jefa shugabannin Saudiyar cikin tsaka mai wuya.

Ita dai Saudiya ta yaba da matakan da aka dauka na kulla yarjejeniyar kawo karshen yakin, amma kuma ta bukaci janye daukacin dakarun Isra'ila dake yankunan Falasdinawa.

Saudiya ta dakatar da tattaunawar farfado da hulda da Isra'ila ne tun farkon barkewar wannan yaki, yayin da ta ci gaba da bayyana adawar ta da yadda sojojin Isra'il ake hallaka Falasdinawa ba tare da kaukautawa ba.

Ga ita Saudiya, abu mafi kankanta shine sanya wa'adi na lokacin da za'a dauka domin ganin an tabbatar da kasar Falasdinu abinda zai bata damar dawo da hulda da Isra'ila.

Shugaba Trump a lokacin mulkinsa na farko ya bayyana irin goyan bayan da yake da shi ga Isra'ila lokacin da ya mayar da ofishin jakadancin kasarsa zuwa Birnin Kudus tare da kaddamar da wani shirin sulhu da ya kira Abrahama Accord wanda kasashe irin su Daular Larabawa da Morocco da kuma Bahrain suka amince da shi.

Ana ganin cewar Trump zai ci gaba da wannan shiri a wa'adinsa na 2 da zai fara aiki gobe litinin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)