Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ne ya buƙaci a gudanar da taron da ke gudana a birnin Riyadh, wanda ke cikin yarjejeniyar majalisar na yaƙi da kwararowar hamada da kuma tunkarar matsalar fari.
Masu fafutukar kare muhalli sun zargi Saudiya wacce ke kan gaba wajen fitar da man fetur a duniya, da ƙoƙarin yiwa yunƙurin rage yawan amfani da makamashi mai gurbata muhalli ƙafar ungulu, a lokacin taron sauyin yanayi na Cop29 da ya gudana a watan daya gabata a Azerbaijan.
A lokacin taron yaƙi da gurgusowar hamada da aka yi a Cote d’Ivoire a shekarar 2022, an cimma yarjejeniyar ganin an matsa kaimi wajen kwato kadada biliyan daya da hamada ta mamaye nan da shekarar 2030.
Taron kwararowar Hamada na COP15 da ya gudana a Abidjan, na ƙasar Cote d’Ivoire. REUTERS - LUC GNAGOSai dai taron wanda ya haɗa ƙasashe 196 da ƙungiyar Tarayyar Turai, a yanzu ya ce dole ne a yi ƙoƙarin ganin an kwato kadada biliyan 1 da rabi 5 nan da wancan wa’adi da aka ɗiba a baya, domin magance matsalolin da ke haddasa fari.
Saudiya na shirin ganin ta kwato kusan kadada miliyan 40 da matsalar kwararowar hamada ta mamaye, duk da cewa bata bayyana lokacin data kayyade don yin hakan ba, ko da yake ana sa ran za ta kwato miliyoyin kadada nan da shekarar 2030.
Kawo yanzu dai, Saudiya ta samu nasarar kuɓutar da kadada dubu dari 2 da 40, ta hanyar amfani da wasu matakai da suka hada da hana sare itatuwa ba bisa ka'ida ba da kuma faɗaɗa yawan wuraren shakatawar da ake dasu a ƙasar daga 19 a shekarar 2016 zuwa sama da 500 a yanzu.
Taron wanda za a kammala a ranar 13 ga wannan watan, zai samu halartar masana da dama, daga ciki kuwa har da shugaban Faransa Emmanuel Macron, wanda ake saran ya halarci taron a gobe Talata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI