Saudiya da Faransa sun ƙulla sabbin yarjeniyoyi yayin ziyarar Macron a Riyadh

Saudiya da Faransa sun ƙulla sabbin yarjeniyoyi yayin ziyarar Macron a Riyadh

Da yammacin jiya Litinin ne Macron ya isa birnin Riyadh inda ya samu tarba ta alfarma, ziyarar da shugaban na Faransa zai shafe kwanaki 3 a ƙasar ta Saudi Arabia, kuma tuni ya gana tare da yin doguwar tattaunawa da Yarima Salman, a wani yanayi da balaguron na shi ke zuwa a dai dai lokacin da rikicin siyasa can a cikin gida ke barazana ga mulkinsa, dai dai lokacin da majalisa ke shirin kaɗa mishi ƙuri’ar yankan ƙauna.

Bayan ganawar shugabannin biyu ne, ofishin Yarima Salman da kansa ya fitar da sanarwar ƙulla yarjejeniyar da Faransa, yarjejeniyar da ta ƙunshi ƙololuwar ƙawancen tsaro baya ga abin da ya shafi makamashi da kuma musayar al’adu tsakanin ƙasashen biyu.

Kazalika, ƙarƙashin yarjeniyoyin akwai kuma tanadin wani yunƙurin magance rikice-rikicen da yankin gabas ta tsakiya ke fama da shi, musamman a Gaza da kuma Lebanon baya ga rikicin Syria a baya-bayan nan.

Shugabannin biyu sun amince da haɗa ƙarfi wajen yin dukkan mai yiwuwa da nufin kawo zaman lafiya a yankin na ƙasashen Larabawa, ciki kuwa har da ganin sun tabbatar da ɓangarorin Isra’ila sa Hezbollah sun mutunta tanade-tanaden da ke ƙunshe a yarjejeniyarsu ta tsagaita wuta.

Bugu da ƙari Mohammed bin Salman da Emmanuel Macron sun kuma buƙaci gwamnatin riƙon ƙwarya a Lebanon ta jagoranci gudanar da sahihin zaɓe don komawar ƙasar kan turbar demokradiyya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)