
Watan mai tsarki, wanda a cikinsa ɗaruruwan miliyan al’ummar Musulmi a fadin duniya ke yin azumi, bisa al’ada yana farawa ne da ganin jinijirin watan Ramadan.
Sauran ƙasashen yankin tekun Fasha, waɗanda akasari al’umarsu mabiya mazahabar Sunni ne, sun bi sahun Saudiyya makwafciyarsu, wajen ayyana ganin watan Ramadan a jiya Juma’a.
Kamfanin dillancin labarai na Saudiyya ya wallafa a shafinsa na X cewa ‘kotun ƙolin ƙasa ta yaanke cewa za a fara azumin watan Ramadan a gobe Asabar’.
Algeria, Masar da Jordan da Libya, Yankuna n Falaɗinawa, Sudan da Tunisia sun sanar da cewa su ma za su fara azumtar watan Ramadan a wannan Asabar.
Amma ofisoshin jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, da fitaccen malamin Shi’a na Iraq, Ayatollah Ali al-Sistani, ssun ayyana cewa sai a ranar Lahadi su da mabiyansu za su fara azumi.
A ƙasar Morocco ce kawai mabiya mazahabar Sunni za su fara azumi a ranar Lahadi, kamar yadda ma’aikatar kula da harkokin addinin Musulinci ta ƙasar ta sanar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI