Hukumar Cyber Security ta kasar Amurka ta ja kunnen cewa satar bayanai ta yanar gizo ka iya karuwa a Amurka da fadin duniya.
Hukumar ta zargi masu satar bayanai ta yanar gizo a Rasha da yunkurin shirin kutse cikin bayanan kanfutocin al’umma.
Hukumar Tsaro Cybersecurity (CISA) ta sanar da cewa masu satar bayanai a yanar gizon na shirin yin kutse ta yarda ba za a taba ganewa ba.