Sarkin Jordan Abdullah na II ya bayyana cewa ya kamata a dauki kwararan matakai bisa adalci domin magance rikicin Falasdin, sabanin haka yankin ba zai taba samun sukuni da zaman lafiya ba.
Sarki Abdullah, a jawabin da ya yi ga kanfanin dillancin labaran kasarsa ta Petra ya bayyana cewa hanya daya ce tilo wacce za a bi domin kawo karshen rikicin Falasdin-Isra'ila waccanan hanyar ita ce kafa kasa biyu tsakaninsu.
Sarkin Jordan ya bayyana ci gaba da kasancewa tara da Falasdinawa kuma zai ci gaba da bayar da dukkanin gudunmowa domin Falasdinawa su dawo da yankinsu kamar yadda suke a shekararr 1967 da kuma tabbatar da Gabashin Kudus a matsayar babban birnin kasarsu.
Ya kara da cewa "Matukar ba a samar da mafita mai kwari bisa dokin adalci ga Falasdinawa ba; ba a taba zama lafiya a yankin da ma a duniya baki daya." Sarki Abdullah dake bayyana haka ya jaddada cewa mafitar ya kamata ta cika dukkan hakkokin 'yan uwanmu Falasdinawa.
Tare da jaddada cewa matakan kasarsa game da batun Falasdinawa ba zai canza ba, Abdullah ya kara da cewa, "Batun Falasdinu batu ne mai muhinmanci ga Jordan."
Sarki Abdullah ya bayyana cewa Jordan za ta ci gaba da kula da kadarorin gidauniyar Musulmi da Kirista a Kudus, kuma za su yi duk kokarin kare asalin Larabawa, Islama da Kiristanci da kuma tsarkakkun wurare a Kudus.