Sarki Abdullah na II na kasar Jordan ya bayyana cewa take hakki da Isra’ila ke yiwa Falasdinawa na haifar da tsattsauran ra’ayi wanda ke barazana ga tsaro.
A cewar bayanin da Masarautar Jordan ta yi, Abdullah na II ya yi magana a taron "Christchurch Call to Action" kan yaki da ta'addanci da tsattsauran ra'ayi na kasa da kasa, wanda aka shirya ta hanyar tattaunawa ta bidiyo konferans.
Da yake bayyana cewa take-taken Isra’ila kan Masallacin Al-Aqsa da Falasdinawan da ke gabashin Kudus, iza wutar tsattsauran ra’ayi da karfafa kalaman nuna kiyayya na barazana ga tsaro, Sarki Abdullah ya yi gargadin cewa rashin samar da cikakkiyar hanyar da za ta dace da batun Falasdinu da Isra’ila zai haifar da mummunan sakamako.