Sanatocin Amurka sun yi kira da a tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Falasdinu

Sanatocin Amurka sun yi kira da a tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Falasdinu

Sanatocin Amurka 28 sun yi kira da a tsagaita wuta cikin gaggawa don hana ci gaban tashin hankali da asarar rayuka a Falasdinu da Isra'ila.

Sanatoci daga Jam’iyyar Democrat 28 karkashin jagorancin Sanatan jihar Georgia, Bayahude na farko, Jon Ossoff sun fitar da wata sanarwar hadin gwiwa dangane da rikicin da ke kara ta'azzara a kwanan nan a Falasdinu da Isra'ila.

A cikin sanarwar an bayyana cewa, "Muna kira da a tsagaita wuta cikin gaggawa don hana ci gaban tashin hankali da kuma asarar rayukan fararen hula a rikicin da ke faruwa a yankunan Isra'ila da Falasdinawa." 


News Source:   ()