Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya bayyana cewa tashin hankali tsakanin kasarsa da Turkiyya ya ragu a makwannin da suka gabata.
Emmanuel Macron ya bayyana a wani taron manema labarai a Brussels, babban birnin Belgium inda aka gudanar da taron kungiyar Tarayyar Turai (EU), cewa tashin hankali tsakanin Paris da Ankara ya ragu a makonnin da suka gabata.
Macron ya lura da cewa kasashen EU za su “kasance cikin shiri” a lokacin bazara, kuma za su sake shiga hadin gwiwa da Turkiyya.