Saudiyya ta sanar da cewa a wannan shekarar za a gudanar da aikin Hajji ne karkashin matakan kiwon lafiya da tsaro na musamman don yaki da barkewar Covid-19.
A cikin wata rubutacciyar sanarwa da Ma'aikatar Aikin Hajji da Umra ta fitar, an bayyana cewa an shirya gudanar da aikin Hajji ne a bana ta hanyar kare lafiyar mahajjata kuma da la'akari da saukin ibada kuma a karkashin matakan kiwon lafiya na musamman.
A cikin sanarwar, an rawaito cewa za a raba bayanai game da yanayin aikin Hajji da kuma matakan na kariya a nan gaba.
Saudiyya ta karbi mahajjata na cikin gida da kalilan daga kasashen waje a bara saboda barkewar cutar Covid-19.