Ministan Harkokin Wajen Labanan, Charbel Wehbe ya musanta labaran da ke cewa Turkiyya ta tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar inda ya bayyana cewar kasashen biyu suna da dangantakar abokantaka.
Wehbe ya fitar da sanarwa a jaridar ”Nida el-Vatan" da aka buga a kasar inda ya ce,
"Turkiyya ƙasa ce mai kawance da Labanan. Labanan tana da allakar ƙawance da Turkiyya. Wehbe da ya ke karin haske kan batun ya ce idan aka kalli batun a yanayi mai tattare da fata, babu wani yanayi na rikici tsakanin Turkiyya da Faransa.
Da yake nuni da cewa kawancen tsakanin Turkiyya da Labanan bata dauki wata yanayi daban ba, Ministan Labanan Wehbe ya lura da cewa a koda yaushe kasashen biyu suna hulda.
"Bayanan da ke cewa Turkiyya ta sa baki a Arewacin Labanan kuma tana goyon bayan wasu kungiyoyin 'yan Sunni ba gaskiya ba ne."
Bayan fashewar abubuwa a Tashar Beirut a watan Agusta, Turkiyya ta mika taimako ga mabukata a Labanan.