Sanarwa daga Amurka game da harin da gwamnatin Assad ta kai da guba

Sanarwa daga Amurka game da harin da gwamnatin Assad ta kai da guba

Amurka ta yi nuni da harin makami mai guba da gwamnatin Assad ta kai yankin Ghouta na Gabashin Siriya a ranar cika shekara 8 da afkuwar lamarin, wanda ya kashe fararen hula sama da 1400.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka Ned Price ya fada a cikin wata sanarwa a ranar cika shekaru 8 da kai harin cewa “Gwamnatin Assad ta yi amfani da makamai masu guba kan al’ummar Siriya akalla sau 50 tun farkon yakin.”

Da yake sake yin kira ga gwamnatin da ta aiyana kuma ta lalata makamanta masu guba daidai da dokokin kasa da kasa, Price ya bayyana cewa Amurka ta yi Allah wadai da amfani da makamai masu guba.

Da yake jaddada cewa ba zai yiwu ba a bar wadanda ke amfani da makamai masu guba ba tare da hukuntasu ba, Price ya bayyana cewa dole ne kuma gwamnatin ta dauki alhakin kai hari da makamai masu guba da laifukan yaki.


News Source:   ()