Sama da yara miliyan 168 Corona ta hana zuwa makaranta a duniya

Sama da yara miliyan 168 Corona ta hana zuwa makaranta a duniya

Sama da yara miliyan 168 Corona ta hana zuwa makaranta a duniya a shekara dayan da ta gabata.

Asusun Tallafawa Ilimin Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya fitar da wani rahoto game da yadda annobar Corona ta hana yara kanana zuwa makaranta, inda 1 daga cikin yara 7 wato su miliyan 214 bai samu damar samun karatu a aji ba.

Rahoton ya ce, wasu yaran miliyan 168 kuma ba su samu damar zuwa makarantar ba saboda kasancewar makarantun a rufe sakamakon annobar ta Corona.

A kasashe 14 an rufe makarantu tun daga watan Maris din 2020 zuwa Fabrairun 2021, kaso 2 cikin 3 na makarantun na Latin Amurka da Carribean wanda lamarin ya shafi yara miliyan 98.

Kasar Panama ce a kan gaba wajen rufe makarantu na tsawon lokaci, sai El Salvador, Bangaladash da Bolibiya da ke biye mata baya.

Daraktar UNICEF Henrietta Fore ta ce,

"Daliban da ba sa samun darussa a azuzuwa suna kara zama a baya a koyaushe, amma wadanda ba ma sa samun karatun gaba daya su suka fi cutuwa."

Fore ta yi kira da kasashe su bude makarantu nan da nan.


News Source:   ()