A duniya baki daya, cutar Corona (Covid-19) ta yi ajalin sama da mutane dubu 950 da 628. Adadin wadanda suka kamu da cutar kuma ya haura mutane miliyan 30 da dubu 356.
Mutane dubu 1,174 sun sake mutuwa a Indiya wanda ya kawo adadin wadanda cutar ta kashe zuwa dubu 84 da 404 Adadin wadanda suka kamu kuma ya karu da mutane dubu 96 da 424 wanda ya kama miliyan 5,214.
A China da cutar ta kash mutane dubu 4,634, an dakatar da shigar da kayan teku na wani kamfanin Indonesiya saboda samun cutar corona a jikin su.
Rubutacciyar sanarwar da Ma'aikatar Lafiya ta Morocco ta fitar ta ce, Covid-19 ta sake yi ajalin mutane 28 sannan an samu mutane dubu 2,488 dauke da cutar. Ya zuwa yanzu mutane dubu 1,714 cutar ta kashe a kasar inda ta kama jimillar mutane dubu 94,504. An bayyana cewar Ministan Makamashin, Albarkatun Kasa da Muhalli na aksar Aziz Al-Rabbah ya kamu da cutar.
A nahiyar Afirka baki daya mutane 174 sun sake rasa rayukansu a awanni 24 da suka gabata wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu zuwa sama da dubu 33 da 484. Jimillar mutane sama da miliyan 1 da 389 ne sukakamu da Corona a Afirka.