Sama da mutane miliyan 27 da rabi Corona ta kama a duniya baki daya

A duniya baki daya annobar Corona (Covid-19) ta yi ajalin sama da mutane dubu 896 da 926. Adadin wadanda suka kamu kuma sun haura miliyan 27 da rabi, yayinda wadanda suka warke daga cutar suka haura miliyan 19 da dubu 592.

A Indiya adadin wadanda suka mutu ya kusa dubu 73. Sama da mutane miliyan 4.3 ne cutar ta kama a Indiya.

A nahiyar Afirka kuma cutar Corona ta sake yin ajalin mutane 218 wnada ya kawo adadin wadanda ta kashe zuwa sama da dubu 31,575. Adadin wadanda cutar ta kama a nahiyar a awanni 24 da suka gabata ya kai sama da dubu 7, wanda ya kama jimillar masu dauke da ita suka kai kusan miliyan 1.4

Afirka ta Kudu ce ta fi samun rasa rayuka a nahiyar, da mutane sama da dubu 15, sai masar da ke biye mata baya da rasa rayuka dubu sama da dubu biyar da dari biya, Aljeriya kuma na da mutane sama da dubu da dari biyar da suka mutu sakamakon kamuwa da Corona.


News Source:   ()