A duniya baki dayamutane dubu 854 da 775 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar Corona (Covid-19). Ya zuwa yanzu cutar ta kama adadin mutane miliyan 25 da dubu 638, adadin wadanda suka warke kuma ya haura mutane miliyan 17 da dubu 943.
Mutane 819 sun sake mutuwa a Indiya wanda ya kawo adadin wadanda cutar ta kashe a kasar zuwa mutane dubu 65,288. A awanni 24 da suka gabata cutar ta kama mutane dubu 69 da 921, inda jimillar wadanda ta kama a kasar ya kai mutane miliyan 3 da dubu 691 da 167.
A yankin Zirin Gaza da Isra'ila ta rufe hanyoyinsa, an kara wa'adin dokar hana fita waje saboda annobar Corona. Ma'aikatar Lafiya ta Falasdin da ke Gaza, ta sanar da mutuwar mutane mutane 3 da Corona ta kama inda wasu 257 suke kamuwa da cutar.
A nahiyar Afirka kuma, a awanni 24 da suka gabata cutar ta sake kashe mutane 226 wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu zuwa dubu 29,862. A nahiyar gaba daya kuma cutar ta kama jimillar mutane miliyan 1 da dubu 257 da 167. Afirka ta Kudu ce ke kan gaba a nahiyar Afirka wajen rasa rayuka da mutane dubu 14,149 sai Masar da dubu 5,421 inda Aljeriya ke biye mata baya da dubu 1,510.