A duniya baki daya, mutane sama da miliyan 1 da dubu 18 ne suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar Corona. Adadin wadanda suka kamu da cutar kuma ya tashi zuwamiliyan 34 da dubu 166, inda wadanda suka warke suka kai sama da miliyan 25 da dubu 437.
A Indiya mutane dubu 1,181 sun sake mutuwa anda ya kawo adadin wadanda cutar ta kashe a kasar zuwa dubu 98,678. A awanni 24 da suka gabata a kasar mutane dubu 86,821 ne suka sake kamuwa da cutar wanda ya kawo adadin masu dauke da ita ya tashi zuwa miliyan 6 da dubu 312.
A Jamhuriyar Turkawan Arewacin Cyprus, Ministan Lafiya Ali Pilli ya bayyana cewar an dauki kwanaki 65 ba a samu wanda ya kamu da cutar a kasar ba, kma tun daga 10 ga watan Maris zuwa yau cutar ta kashe mutane 4, daga cikin mutane 757 da suka kamu da ita.
A Jordan mutane 61 sun mutu, ana da mutane dubu 11,825 masu dauke da cutar, inda a yanzu za a ude Masallatai da Majami'u. Za a ci gaba da rufe makarantu kasar har nan da makonni 2. A ranar 14 ga watan Satumba ne bayan samun karuwar kamuwa da cutar Corona, gwamnatin Jordan ta rufe Masallatan Juma'a da makarantun kasar.