Sama da mutane miliyan 24 Corona ta kama a duniya baki daya

Sama da mutane miliyan 24 Corona ta kama a duniya baki daya

Ya zuwa yanzu a duniya baki daya sama da mutane dubu 827,816 ne suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar Corona, cutar ta kama jimillar mutane miliyan 24 da dubu 280, inda miliyan 17 da dubu 736 suka warke.

A Spaniya a kwanaki 7 da suka gabata mutane 129 sun sake rasa rayukansu wanda hakan ya kawo adadin wadanda cutar ta kashe zuwa dubu 28,971. Ma'aikatar Lafiya ta Spaniya ta ce a awanni 24 da suka gabata mutane dubu 7,296 cutar ta kama wanda hakan ya kawo adadin wadanda suka kamu zuwa dubu 419 da 849.

A lokacin da ake ta takaddamar komawa makarantu saboda annobar ta corona, baya ga malaman makaranta, dalibai ma sun gudanar da zanga-zanga a kasar.

A awanni 24 da suka gabata mutane 13 sun rasa rayukansu a Italiya, wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu zuwa dubu 35,458. An samu karin mutane dubu 1,367 da suka kamu da cutar inda ake da jimillar masu dauke da ita dubu 262,540.


News Source:   ()