A duniya baki daya, annobar Corona (Covid-19) ta yi ajalin mutane sama da miliyan 1 da dubu 103. Adadin wadanda cutar ta kama kuma sun haura miliyan 29.4.
A awanni 24 da suka gabata mutane 895 sun mutu a Indiya wanda ya kawo adadin wadanda cutar ta kashe a kasar zuwa sama da dubu 112,161. A wannan loakci kuma cutar ta sake kama mutane dubu 63 da 371 wanda ya kawo adadin wadanda ta kama zuwa miliyan 7.4.
Ministan Lafiya na Jamhuriyar Turkawan Arewacin Cyprus Ali Pilli ya gargadi 'yan kasar kan kar su ziyarci Kudancin Cyprus Bangaren Girka idan ba ta kama dole ba saboda yadda cutar ke karuwa a yankin. An samu samun mutane 93 dauke da cutar a Kudancin Cyprus wanda wannan ne adadi mafi yawa da aka samu a rana guda tun bayan bullar cutar, kuma ya zuwa yanzu mutane dubu 2,274 ta kama a yankin.