A duniya baki daya, mutane sama da dubu 900,900 ne annobar Corona (Covid-19) ta yi ajali. Cutar ta kama sama da mutane miliyan 27.7. Wadanda suka warke kuma sun kusa mutane miliyan 20.
A awanni 24 da suka gabata a kasar Indiya, mutane 1,115 sun sake rasa rayukansu wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu zuwa sama da dubu 89 da 300. Jimillar mutane miliyan 4.3 ne cutar ta kama a Indiya.
A Jamhuriyar Turkawan Arewacin Cyprus an tsaurara matakan yaki da Corona sakamakon yadda masu kamuwa da cutar suke kara yawa a 'yan kwanakin nan. An rufe dukan wajen holewa, gidajen rawa da gidajen caca har nan da 1 ga watan Oktoba. An soke tarukan siyasa har sai nan da 1 ga Oktoba. Haka zalika dalibai za su ci gaba da kasancewa a gida har zuwa wannan lokaci.