A duniya baki daya, sama da mutane dubu dari takwas da ashirin da uku da dari takwas da hamsin (823,850) ne suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar Corona (Covid-19).
A Indiya da ta zama kasa ta 3 mafi yawan masu dauke da cutar, mutane dubu 59 da 612 ne suka mutu daga cikin mutum miliyan 3 da dubu 234 da 474 da ta kama.
A nahiyar Afirka baki daya mutane 283 sun sake mutuwa wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu zuwa dubu 28 da 334. Adadin wadanda cutar ta kama a Afirka ya kai mutum miliyan 1 da dubu 207 da 623. Ya zuwa yanzu a Afirka, kasar Afirka ta Kudu ce ta fi samun wadanda suka mutu inda ta ke da mutane dubu 13 da 308 sai Masar da ke da dubu 5 da 298 inda Aljeriya ta ke biye mata baya da dubu 1 da 466.