Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya bayyana cewar bikin babban nasarar ranar 30 ga watan Agusta na sake bayyana duniya cewa wacannan kasar mallakar al'ummanmu ce.
Shugaba Erdoğan ya yada sakon zagayowar shekara ta 98 da samun nasaraa ranar 30 ga watan Agusta.
A yayinda Erdogan ke yiwa dukkanin Turkawa murnar bikin ranar Nasara ta 30 ga watan Aguska ya bayyana cewa,
"A gwagwarmayar da Gazi Mustafa Kemal Atatürk ya jagoranta a shekarar 1919 a Samsun, tare da kwandojinsa sun samu babban nasara mai dorewa a ranar 30 ga watan Agusta. Wannan nasarar ta kasance cikin tarihin kasarmu mai muhinmanci"
Shugaba Erdogan ya kara da cewa ba abin mamaki bane ganin yadda wadanda suka yi yunkurin mamaye kasarmu a karnin baya suka kasance daya da wadanda ke yunkurin fitar damu daga Bahar Rum.
Ya kara da cewa ina mai matukar mika godiya ga jagoran wanda ya kubutar da kasarmu Gazi Mustafa Kemal Atatürk da abokansa da kuma addu'ar samun rahamar Allah ga wadanda suka rigamu gidan gaskiya a yayin gwagwarmayar kare kasarmu. Ina mai yiwa dukkanin al'umman kasarmu barka da bikin nasarar ranar 30 ga watan Agusta.