Sheik Abduljabbar Nasir Kabara a wata gajeruwar bayanin da ya yi ya nemi afuwan al'umman Musulmi akan kalaman batancin da ake cewa ya yi duk da yana ci gaba da cewa ba’a fahinceshi ba.
A jawabin da ya fara da yin sallama ta addinin Musulunci da ya bayyana a matsayin sako na musamman ga al’umman Musulmi, maza da mata, yara da manya. In da yake cewa,
“Ma’anar wannan sakon da manufarsa shi ne kan wadannan kalmomi da aka daddatse wanda ni ina cewa natijarsu ta fito ne daga Hadisai na karya kuma ni ina yaki dasu don kare darajar annabi”
Ya kara da cewa masu sauraro hankalinsu ya rabu sabili da daddatse bayanan da aka yi ana cewa shi ne ya fada, amma wadanda ke binsa sun gane abinda yake nufi sai dai wadanda iya datsewar suka ji ko suka kalli mukabalan da aka yi basu fahinceshi ba.
Shehin Malamin ya bayyana cewa sai an hada hadisai kusan goma ko fiye da hakan ne zasu iya fitar da natijan da yake nufi, ba wai guda daya bane kawai.
Ina cewa al’umman Musulmi idan wadanan maganganu daga ni suke babu su ga litattafan Hadisi ina mai tuba da neman gafarar Allah, amma in a cikin litattfancan suke ya kamata mu tashi tsaye mu tsarkake addininmu.
Daga karshe ya yi fatan Allah ya hada kan Musulmi Ya gusar da gaba a tsakaninmu, ya kuma rufe da cewa Wassalamu Alaikum Wa’tala Wabarakatuhu.