Sake mayar da Hagia Sophia Masallaci kafa babban tarihi ne

Sake mayar da Hagia Sophia Masallaci kafa babban tarihi ne

Tarayyar Malaman Mağrip Larabawa sun bayyana cewa sake mayar da Hagia Sophia masallaci "kafa babban tarihi ne"

Sanarwar da sharhin da ta fito daga tarayyar malaman addinin Islama daga kasashen Libiya, Tunusiya, Aljeriya, Morocco da Moritaniya ta nuna cewa,

"Muna masu tara al'umman Turkawa, Shugaba Recep Tayyip Erdoğan da dukkanin Musulmi murnar mayar da Hagia Sophia gurin ibadan Allah. Wannan kafa babban tarihi ne"

Sanarwar ta kara da cewa masallaci guri ne na ibadan musulmi sabili da haka kada wanda ya nemi yin yunkurin sukar wannan matakin.

"Muna addu'a da rokon Allah ya nuna muna irin wannan rana akan Masjid Aksa lokacin da za'a kubutar dashi daga hannun yahudawa"

 


News Source:   www.trt.net.tr