Janet Yellen, Sakatariyar Baitulmalin Amurka, a cikin kimantawar sabbin kudin yanar gizo na Stablecoins, ɗaya daga cikin nau'ikan kuɗin yanar gizo ta ce "Dole ne a hanzarta yin aiki don tsarin da ya dace."
A cewar sanarwar da Ma’aikatar Baitulmalin Amurka ta fitar, Yellen ta gudanar da taron Kungiyar Hadin Gwiwar Kasuwani tare da halartar Ofishin Kula da Kudi da kuma Hukumar Inshora ta Tarayya don tattaunawa kan Stablecoins.
A taron an yi magana kan saurin ci gaban Stablecoins, ɗaya daga cikin nau'ikan kudaden yanar gizo kuma da damar amfani da su azaman hanyar biyan kuɗi, tare da haɗarin da masu amfani da su ke iya fuskanta, tsarin kuɗi da tsaron ƙasa.
Yellen ta jaddada bukatar yin aiki cikin sauri don tsarin doka mai dacewa na Stablecoins.