Daya daga cikin wadanda suka kafa kamfanin BioNTech da ke Jamus kuma suka samar da allurar riga-kafin Covid-19 Farfesa Ugur Sahin ya bayyana cewa, annobar ta janyo matsalar da za a dauki shekaru 10 ana fama da ita.
Ya ce, "Mun samar da allurarmu don amfanin mutane miliyan 10 amma har yanzu akwai abubuwan da za a yi nasara a kansu da yawa. Muna son allurarmu ta isa ga kowa a bayan kasa."
Bankin Duniya, Asusun Bayar da Lamuni na Duniya da Kungiyar Turkawa Ma'aikata sun shirya taro ta hanyar sadarwar bidiyo tare da Ugur Sahin da matarsa Ozlem Tureci inda aka tattauna kan "Hadin Kai Wajen Yaki da Annoba".
Sahin ya nuna muhimmancin hadin kai wajen yaki da annobar inda ya kuma ce,
"A bayyane ta ke karara cewar wannan cutar za ta zauna tare da mu tsawon lokaci. Wannan ba matsala ce da za ta wuce a 2021 da 2022 ba. Matsala ce da za a dauki shekaru 10 ana fama da ita."
Ozlem Tureci ta bayyana cewa, suna son yin adalci wajen sayar da allurar riga-kafin da suke samarwa, kuma hadin kan kasa da kasa na da muhimmanci wajen tabbatar da hakan.