Sabuwar Gabas ta Tsakiya

Sabuwar Gabas ta Tsakiya

Masu saurarenmu barkamu da wannan lokaci a cikin wani sabon shirinmu na sharhin al'amurran yau da kullum. A wannan makon akan sharhin Gabas ta Tsakiya mun kasance tare da Mal. Can ACUN manazarcin harkokin waje a Gidauniyyar Nazarin Siyasa, Tattalin Arziki da Hallayar Dan Adam wato SETA…

Haķiķa sauyin mulkin da aka samu a Amurka, ya sauya lamurra da dama a Gabas ta Tsakiya. Musanman yadda yariman Saudiyya mai jiran gado, ya rasa irin cikekken goyon bayan da Trump ke bashi, ya tilastu da sauya tsarukansa na yau da kullum. Haka kuma, ganin yadda Amurka ta koma kan teburin sulhu da lran akan harkokin nukiliya ya sanya lsra'ila daukar matakan kin kari dake tayar da zaune tsaye. Ita kuwa Turkiyya ta na kara daukar sabbin matakan cimma bukatunta ne.

Gabas ta Tsakiya, ta kasance yanki mai muhinmanci a doron kasa. Yanki ne dai, da ya kasance cikin rudani maimakon kwanciyar hankali. Abin bakin ciki ne yadda yankin ya kasance wurin baiwa hamutta iska tsakanin kasashe masu karfi. Musanman yadda wadanan kasashen ke gwagwarmaya da juna wajen mallakar ikon yankin. Turkiyya duk da ba ta kasance daya daga cikin kasashen Gabas ta Tsakiya ba, takan shafu da dukkan abubuwan dake faruwa a yankin. Akan hakan ne ya sanya ta tilastu da sauya rawar da take takawa a yankin musanman bayan sauyin mulki a Amurka. Bugu da kari,  musanman ma yadda mulkin Biden ya koma kan teburin sulhu da lran akan harkokin nukiliya da kuma rage matsin lamba akanta, Salafi kamar su yarimomin Saudiyya da na Hadaddiyar Daular Larabawa suka rasa irin goyon bayan da Trump ya kasance yana basu.

Israila da kasashen yankin Gulf na cikin fargaba akan wannan sauyin da aka samu. Sai dai suna yunkurin daukar matakai na daban akan lamurran dake faruwa a halin yanzu. Matakan da lsra'ila ta dauka basu kasance ba face da zummar rage karfin matakan da Amurka-lran suka fara ayyanarwa. Iran dai na yunkurin kara kwanjinta a ciki da waje kamar irin kasar Siriya. Haka kuma a yankin Gabas ta Tsakiya da Bahar Maliya kasashen biyu na kalubalantar jiragen ruwan juna. Ala kulli halin ana ganin dai lran ta zabi kaucewa tsokanar da lsra'ila ke yi a wannan lokacin.

 

Kasashen yankin Gulf da suka rasa cikkakkiyar goyon bayan da suka samu a lokacin mulkin Trump sun tilastu da su sake sabbin tsari a kasashensu. Da farko dai sun ja da baya daga takunkuman da suka kakkabawa kasar Katar da kuma ma daukar matakan daidaitawa da ita. Haka kuma, sun fara kusantar Turkiyya cikin ruwan sanyi. Duk da dai ba a fara harkokin siyasa masu kwari ba amma alamomi sun nuna cewa kasashen na shirin inganta dangantaka tsakaninsu.

Turkiyya wacce ta kasance muhimmiyar kasa a yankin, ba zata kasance ware a wannan shirin sauyin ba. Kasashen da suka kalubalanci Turkiyya a lokacin mulkin Trump sun fara daukar matakan shiryawa da ita. A yayinda shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ke cigaba da tattaunawa da Sarkin Saudiyya Salman Bin Abdulaziz ta wayar tarho,  haka kuma ake cigaba da daukar matakan daidaitawa da Masar. Tawaga daga Turkiyya ta gudanar da muhimmiyar tattaunawa a Alkahira kuma ga dukkan alamu ƙasashen biyu sun mai da hankali kan abubuwan da suka dace don fita daga lamurran da ba zasu haifa musu ýaýa masu idanuwa ba. Hakika wannan ya taimakawa samar da lumana a Libiya.

Dangane da waɗannan ci gaban, a bayyane yake cewa muna cikin sabon tsari wanda zai shafi matsayin siyasa na ƙasashe a Gabas ta Tsakiya. Dukkanin kasashen ana ganin cewa zasu dauki matakan sauya tsare-tsarensu. A dan lokaci za'a iya dakatar da yaki ta sigar wakilcin da aka jima ana yi a yankin. Matakan da lran da lsra'ila zasu dauka a wannan lokacin ya na da muhinmanci kwarai da gaske. Rikicin dake tsakanin lran da lsra'ila idan ya yawaita zai iya shafar yankin baki daya. Ita kuwa Turkiyya ana ganin za ta cigaba da yaki da ta'addanci da take yi a iyakokin lraki da Siriya.

Wannan sharhin Mal. Can ACUN ne manazarcin harkokin waje a Gidauniyar Nazarin Siyasa, Tattalin Arziki da Hallayar Dan Adam wato SETA dake nan Ankara babban birnin ķasar  Turkiyya. Ku huta lafiya…


News Source:   ()