Shugaban ya rantsar da ministocin da adadinsu ya kai 109 inda suka kama aiki nan take.
Shugaban kasar ta Indonesia Prabowo Subianto Ya bada sanarwar jerin ministocin nasa ne a yammacin Lahadin da ta gabata tare da kafa majalisar zartaswar kasar da ta kunshi ministocinsa, mataimakansu da kuma shugabannin hukumomin kasar. An kuma rantsar da ministocin a yau litinin.
Subianto ya zama shugaban kasa na takwas a kudu maso gabashin Asiya mafi karfin tattalin arziki a ranar Lahadi.
Majalisar ministocin Subianto ita ce mafi girma tun ta shekarar 1966 lokacin da Shugaban kasar na farko Sukarno ya naɗa ministoci 132 a yayin da ake cikin wani ruɗanin siyasa, bayan yunkurin juyin mulkin da aka yi ba tare da nasara ba a 1965.
Subianton dai a baya ya bayyana cewa yana bukatar kafa gwamnati mai karfin gaske, duk da cewa manazarta na ganin tumbatsar majalisar ministocin nasa zai yiwa gwamnatinsa karan tsaye.
Majalisar ministocin ta hadin gwaiwa ce wadde ta kunshi jam'iyyu 7 da suka ba da goyon bayansu a zaben da ya gudana a watan Fabrairu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI