Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya (WHO) ta sanar da cewa sabon nau'in kwayar cutar Korona ta Delta wanda aka fara gani a Indiya, an ci karo da shi a kusan kasashe da yankuna 100.
A cewar labarai na Gidan Talabijin na (CGTN), Sakatare-Janar na hukumar WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya yi gargadin cewa an ga nau'ikan korona na Delta, wanda aka gano ana saurin yada shi cikin sauki a kasashe akalla 98.
Ghebreyesus ya bayyana cewa nau'in yana yaduwa cikin sauri a kasashen da ke fama da karancin allurar rigakafi, Ghebreyesus ya lura cewa nau'in Delta yana da hadari kuma yana ci gaba da karuwa da kuma canzawa.