Bayan sabon nau'in kwayar cutar Corona na Delta, an sake samun bullar wani sabon nau'in mai suna Lambda.
Sabon nau'in da aka baiwa suna Lambda ya fara bulla a kasar Peru.
Ya zuwa yanzu an samu sabon nau'in cutar ta Corona a kasashen duniya 30.
Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya WHO ta sanar da cewa, tun daga watan Afrilu ake ta ganin wannan nau'i wanda shi ne kaso 81 na sabbin kamuwa da cutar da aka samu.
Masanan kimiyya na fargaba kan akwai yiwuwar wannan sabon nau'i ya fi yaduwa cikin sauri kuma ba zai ji riga-kafi ba.