
Gwamnatin Rwanda na zargin Belgium da ɗaukar bangare a rikicin gabashin Jamhuriyar Dimokaraɗiyyar Congo da ‘yan tawayen M23.
Ƙasar Belgium ta sha yin kira a 'yan makonnin da suka gabata da a mutunta yankin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo.
Rwanda, wacce ta musanta goyon bayan M23, ta ce Belgium na gudanar da wani gagarumin shiri na toshe hanyoyin samun kudaden raya kasar.
A cewar Rwanda, matakin na Belgium, bashi da maraba da zagon kasa ga kokarin shiga tsakanin da ake yi, don ganin an kawo ƙarshen rikicin.
Sakamakon haka, Rwanda ta yanke shawarar watsi da yarjejeniyar tallafi da kuma aikin jin ƙai da kasashen biyu suka cimma a shekarar 2024, wadda za ta kai har shekarar 2029.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI