Rundunonin soji 2 da ke karkashin gwamnatin Iraki sun koma yankin Sincar da ke karkashin jihar Mosul.
Labaran da jaridun Iraki suka fitar sun bayyana cewar, Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta mayar da rundunonin 'yan sanda 2 zuwa Sİncar.
Gwamnatin Iraki ta ce helkwatar 'yan sandan kasar ce za ta samar da tsaron Sİncar.
Bagdat da Erbil sun sanya hannu kan wata doka da ta tanadi kwashe 'yan ta'addar PKK daga Sincar.