Shugaban kasar Iran Hasan Ruhani ya bayyana cewa shugaban kasar Amurka mai barin gado Donald Trump bai da babbanci da tuntsararren shugaban kasar Iraki Saddam Hussaini.
"Kamar dai yadda Saddam ya yaki Iran har na tsawon shekaru 8 daga bisani aka rusa shi; haka ne dai Trump ya yaki Iran a fannin tattalin arziki na shekaru 3 wanda shi ma mako mai zuwa zai sauka kuma tabbas zai kasance mutum mafi rashin mutunci a tarihi"
Shugaba Ruhani da ya halarci taron bude wasu ayyuka a jihar yammacin Azabaijan a kasar Iran ya yi sharhi akan kashe kwamandan kare Kudus Kasim Sulaiman da kuma irin salon mulkin Trump.
Ya bayyana cewa Trump ya shirya kisan gilla da dama amma kashe Kasim Sulaiman da injiniya Abu Mahdi abu ne wanda ba za'a taba mantawa dasu ba kuma Iran za ta dauki fansa a lokacin da ya dace.
Haka kuma Ruhani ya kara da cewa wadanda ke bayyana gazawar Iran akan fuskantar Amurka karya suke yi, wadanda ke ganin haka 'yan amshin shatan Amurka ne domin Iran tsaye take tsayin daka akan harkokinta na yau da kullun.