Shugaban kasar Iran Hassan Ruhani ya bayyana cewa sabuwar gwamnatin Amurka karkashin Joe Biden za ta dawo akan yarjejeniyar da aka yi da ita kuma takunkuman da kasar ta kakkaba zasu gushe.
A yayinda Ruhani ke jawabi akan bude wasu ayyukan ma'aikatan cikin gidan kasar Iran ta yanar gizo, ya yi sharhi akan takunkuman da Amurka ta kakkabawa Iran.
Ruhani wanda ya yi kira ga al'umman kasar da su yi iya kokarinsu wajen ganin takunkuman basu yi nasara ba ya kara da cewa " Tsayin dakan da Iran ta yi zai sanya sabuwar gwamnati mai zuwa ta bayar da wuya domin bori ya hau" Ba ni da shakkan cewa Amurka za ta dawo akan yarjejeniyar da aka yi da ita kuma takunkuman da ta kakakba ba zasu yi nasara ba"