Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya yi kira ga shugaban Amurka Joe Biden da ya aiwatar da yarjejeniyar nukiliya cikin dan kankanen lokaci.
Rouhani ya yi bayani game da yarjejeniyar nukiliyar da kuma matsayin Amurka bayan taron Majalisar Ministocin a Tehran, babban birnin kasar.
Rouhani ya yi kira ga Biden da ya hanzarta aiwatar da yarjejeniyar nukiliyar.
"Biden yana cin amanar kuri'un jama'arsa idan har ya kasance mai sassauci game da aiwatar da yarjejeniyar nukiliyar. Saboda sun jefa kuri'a a kan hakan, kuma ya zo ne don ya dage takunkumin kuma ya gyara kurakurai. Sannan ya sha nanata cewa ya amince da yarjejeniya kuma yana bukatar dawowa da ita"
Rouhani ya ce don sake farfado da yarjejeniyar nukiliyar, ya kamata Amurka da Iran su dauki matakan da suka dace ba tare da bata lokaci ba.
Ya nanata cewa basa ayyanar da ayyukan makaman nukiliya da makaman kare dangi, Rouhani ya ce zarge-zargen da ake yi game da hakan ba su da tushe.