Ronaldo wanda ya taimakawa Brazil lashe kofin duniya a shekarar 1994 da kuma 2002 ya ce zai tsaya takarar zaben da za'ayi a shekarar 2026 domin maye gurbin shugaban dake ci Ednaldo Rodrigues.
Tsohon 'dan wasan ya ce dalilin bayyana sha'awar jagorancin hukumar kwallon kafar shi ne domin dawo da kimar Brazil a idan duniya.
Tsohon tauraron da ya yiwa kungiyoyi irin su Barcelona da Inter Milan da kuma Real Madrid wasanni lokacin ganiyarsa ya ce zai sayar da hannun jarin da yake da shi a kungiyar Real Valladoid ta Spain domin ba shi damar tsayawa takarar ba tare da matsala ba.
Ronaldo ya mallaki kashi 90 na hannun jarin kungiyar Cruzeiro dake fafatawa a gasar Brazil kafin ya sayar a wannan shekarar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI