Rikicin da ke tsakanin Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa a tattaunawar kan kason samar da mai na manyan kasashe masu fitar da man fetur a duniya, da ake kira Opec plus, ya bayyanar da matsalolin da ke tsakanin kasashen biyu a fili. Duk da ci gaban kawancen da ke gudana tsakanin kasashen biyu, a gaskiyar lamari akwai rarrabuwar kawuna kan batutuwa da dama har ma da fadace-fadace wadanda suka haifar da muhimman alamomin tambaya game da daidaito a yankin Gulf musamman a ‘yan kwanakin nan.
Akan wannan maudu’in mun kasance tare da Mal. Can ACUN manazarcin harkokin waje a Gidauniyar Nazarin Siyasa, Tattalin Arziki da Hallayar Dan Adam wato SETA..
Kungiyar Opec plus da ta hada da mambobin kungiyar Opec da Rasha ta dauki tsawon lokaci tana kokarin iyakance farashin mai ta hanyar daidaita bukatan man da samar da shi. Musanman a lokacin da Amurka ta kara yawan man da take samarwa daga duwatsu tasirin kayyade farashin man kasashen Opec Plus ya ragu kwarai da gaske. Kodayake an lura cewa suna cikin mawuyacin hali a lamarin samar da daidaiton farashi, membobin sun sami nasarar kiyaye haɗin gwiwar dake tsakaninsu. Koyaya, yunƙurin Hadaddiyar Daular Larabawa don wuce ƙididdigar yawan man da za ta iya samarwar da aka sanya a cikin sabon lissafin da alama ya fusata Saudiyya sosai. Zargin juna ya ci gaba tsakanin kasashen biyu bayan da ministan mai na Saudiyya ya kwatanta Hadaddiyar Daular Larabawa ta wata hanyar da ba a saba gani ba.
Dangane ga sharhin wasu masana; ba wai akan lamarin iyakance fitar da mai na Opec Plus ma kawai ba, akwai ma wasu matsaloli masu yawa tsakanin kasashen biyu. Ga alamu kasashen biyu sun fara samun sabanin ra’ayi game da bautuwan Falasdin, Katar da Yaman.
A zahiri, a lokacin Trump, akwai ƙawancen Hadaddiyar Daular Larabawa da na Saudiyya karkashin jagorancin Isra’ila da yahudawan sahyuniya. Lamurran yankin ya kasance karkashin kawanceceniya. Yariman Abu Dhabi mai jiran gado Muhammad Bin Zayed da yarimar Saudiyya mai jiran gado Muhammad Bin Salman sun yi fice a wajen ayyanar da irin wadanan kawance-kawancen. Sai dai akan harkokin kayyade fitar da mai, yadda bukatun Hadaddiyar Daular Larabawa ke wuce na Saudiyya ya haifar da kalubalantar juna tsakanin masarautun. Musamman a harkokin Falasdin da Yeman kawunan kasashen ya rabu kwarai da gaske. Bayan faduwar Donald Trump zabe da kuma rasa ikon shugaban Isra’ila Benjamin Natinyahu kawancen dake tsakanin wadannan kasashen ma ta fara rugujewa, lamarin da ya sanya Saudiyya fara fafutukan kare muradunta. Yayin da aka yi watsi da matsayar da ke nuna goyon baya ga Isra’ila kan batun Falasdinu, dangantaka da Katar ta daidaita. Haka kuma a Yaman Hadaddiyar Daular Larabawa ta janye daga harkokin kalubalantar Houthi da karfin soja. Yayin da Saudiya kuma ta zargi Hadaddiyar Daular Larabawa da goyon bayan yankin kudu ‘yan aware, duk wadannan ci gaban sun bayyana ne bayan taron Opec +.
A hakikanin gaskiya ba’a tunanin kasashen biyu zasu kalubalanci juna wanda zai kai baiwa hamutta iska, sai dai Saudiyya za ta ci gaba da daukar matakan kare muradunta tare da daukar matakai ita tilo a harkoki da dama. A karshe dai, za’a iya bayyana cewa Muhammad Bin Salman zai kasance shi kadai a ire-iren wadannan harkokin kuma zai dauki nauyin dukkan lamurran da hakan zai haifar.
Wannan sharhin Mal. Can ACUN ne manazarcin harkokin waje a Gidauniyar Nazarin Siyasa, Tattalin Arziki da Halayyar Dan Adam wato SETA dake nan Ankara babban birnin kasar Turkiyya. Ku huta lafiya.