A yayinda aka fara rikici tsakanin Peshmerga da PKK sakamakon tasirin matakan da Turkiyya ta dauka a arewacin lraki, bangarori sun fara janyewa daga kasar Siriya. A lokacin da wadanda ake kira shugabanin PYD/YPG suka fara furucin kalubalantar KDP, ita ma KDP ta mayar da martani ga shugabanin PYD/YPG inda ta bayyana su a matsayin bangaren kungiyar ta'addar PKK a Siriya. Yanzu haka, an rufe kofar iyakar Fishhabur / Semalke, kuma an kame wakilan PYD / YPG a Erbil. An rufe ofisoshin K24 na kungiyar ta'adda ta PKK a yankin Siriya.
Akan wannan maudu'in mun sake kasancewa tare da Mal Can ACUN manazarcin harkokin waje a Gidauniyar Nazarin Siyasa, Tattalin arziki da Hallayar dan Adam wato SETA. ...
A yayinda Turkiyya ke cigaba da daukar matakan soji akan kungiyar ta'addar PKK a arewacin lraki, hukumar leken asirin kasar Turkiyya ta MIT ta cigaba da daukar matakan hadin gwiwa da take magance manyan shugabanin yan ta'addan. Gudunmowa ta sama da Peshmerga ke baiwa Turkiyya ya kara bada damar fatattakar yan ta'addan inda suka yi nasarar tarwatsa mambobin kungiyar ta'addar daga yankin da suke da iko. Kungiyar ta'addar da ta fada cikin halin kakanikayi ta kasa katabus ta fara kaiwa Peshmerga hari. A gefe guda, shugabanin KDP na fitar da sanarwar kalubalantar KDP, bugu da kari, akwai ƙoƙari don ƙirƙirar yanayi na matsin lamba ga KDP ta hanyar tattara ra'ayoyin jama'a na Kurdawa da ƙungiyoyi masu zaman kansu masu alaƙa da ƙungiyoyin siyasa da ke tallafawa PKK. A ƙarshe, abubuwan da aka tsara a Turai sun yi ƙoƙari su zama garkuwa ga PKK a yankin, amma nisantar da KRG ta yiwa yunkurin ya haifar da rashin nasararsa.
Ana dai ganin cewa rikicin dake tsakanin KDP da PKK zai iya fara afkuwa a Siriya. A kwanakin baya kungiyar YPG ta kai hari ga barikin Peshmerga dake kan iyaka kuma suka karbe ikon yankin cikin dan lokaci. Bugu da kari, an kona ofisoshin Majalisar Kurdawa ta Kasa (ENKS), wacce ke kusa da KDP, kuma an bayyana cewa kungiyar matasa ta PKK ce ta aikata hakan. A halin yanzu rikicin ya haifar da rufe kofar da ya hade Fishhabur/ Semalka. Bugu da kari, an kame sanannun sunayen da suka kasance wakilan PYD / YPG dake cikin KRG a Erbil. PYD / YPG, kuwa sun mayar da martani ta hanyar rufe ofisoshin K24, sashen yada labarai na KRG, tare da toshe ayyukan rahotonta. Bugu da kari, an shirya kananan zanga-zanga da yawa karkashin wadanda ke goyon bayan kungiyar ta'adda ta PKK da kuma la'antar KDP a yankuna kamar Qamishli da Ayn al-Arab.
A yayinda dai fafatawa tsakanin Peshmerga da PKK ke cigaba da kamari, lamarin ya fara hadawa da kungiyar PYD/YPG dake Siriya, hakan ya kuma haifar da fara sulhu da bangaren kungiyar PKK dake Siriya. Ana ganin cewa ya wajabta ga gwamnatin Kurdawan Iraki da KDP zata cigaba da kalubalantar kungiyar PKK a Siriya. Ya kamata KDP ta ga muhinmancin kokarin da dakarun kasar Turkiyya ke yi ta kuma dauki hakan a lmatsayin dama musanman yadda karfin gwamnatin Kurdawan lraki ta rage kwarai. A halin yanzu dai ana bayyana cewa Peshmerga da KDP sun kafa wata tarihin tallafawa Turkiyya domin yaki da kungiyar ta'addar. Idan har basu yi amfani da wannan damar ba, zasu ci gaba da fuskantar wannan kungiyar ta ta'addanci tare da biyan diyya.
Wannan sharhin Mal. Can ACUN ne manazarcin harkokin waje a Gidauniyar Nazarin Siyasa, Tattalin arziki da Hallayar dan Adam wato SETA dake nan Ankara babban birnin kasar Turkiyya.