Lamurkan soji a kasar Libiya sun dauki sabbin salo a yan kwanakin nan da suka gabata. Taron sulhun da aka gudanar a Morocco da Montreux ya bayyanar da cewa akwai niyar sauya kwamitin firaiminista akan harkokin kasar. A sanadiyar tarzomar siyasa da aka gudanar a Tripoli da Bengazi ne ya sanya janye shugabacin halastacciyar gwamnatin kasar da kuma na bangaren Haftar watau Serrac da Tinni. Bayan bayana yunkurin ajiye mulkin Serrac wanda zai yi a watan Octoba ne kuma kasar ta sake fadawa cikin wani sabon rikicin siyasa da ake gani a halin yanzu.
Akan wannan maudu'in mun kasance tare da Dkt Murat Yesiltas daraktan harkokin tsaro a Gidauniyar Nazarin Siyasa, Tattalin Arziki da Hallayar Dan Adam watau SETA…
A halin yanzu an ganin yadda masu goyawa Hafter baya ke kara kaimin a harkokin ķasar. Da hakan ake ganin suke kokarin kafa kungiyar da zata tabbatar da tsarin siyasar ķasar Libiya. Wannan dai wani abu ne da zai iya sanya siyasar cikin gidan Libiya sake daukar sallon da zata samawa kanta mafita.
A matakin warware matsalar kasar ta hanyar siyasa; taron da shugaban kwamitin zartarwa ta kasar Libiya Halid Mishri ya yi da shugaban majalisar ķasar Akila Salih a Morocco ake ganin za'a iya kawo karshen matsalar kasar. An tabbatar da yadda lamurkan zasu kasance; sun ta'alaka ne akan irin taron da Mishri zai yi Ankara da kuma wanda Haftar da Salih zasu halarta a Alkhahira. Ana dai ganin hadewar Haftar da Salih wadanda basu ga maciji ga juna tilastawar Sisi ne. Taron sulhun Libiya da aka gudanar a Montreux ya bayyanar da irin kwararan matakan siyasa, inda aka bayyana sauya tsarukan siyasar ķasar wanda Serrac da kansa ya bayyana.
Kamar yadda lamurka suka bayyana lamurkan siyasa sun fara tasiri a Libiya. Wadanda ma ke yunkurin mallakar kasar Libiya sun fara fahimtar yadda tsarin siyasar ķasar Libiya ke dada gwabi a kasar. Bugu da kari matakan da Turkiyya da Rasha suka dauka a Libiya na damuwar wasu kasashe da dama. Bayanin da Lavro ya fitar a wannan makon wanda ya yi nuni shirin sulhun da Turkiyya ya ja hankali kwarai da gaske. Musanman inda ya bayyana cewa ķasashen biyu nada abu daya a Libiya watau sojojinsu.
Hadakar Haftar da Salih da masu goya musu baya bata kasance akan tsarin siyasar ķasar Libiya ba face kawo karshen kasancewar Turkiyya da Rasha a kasar. Bugu da kari kalubalantar Rasha da Amurka take yi a Libiya ya fito fili ne ganin irin bayanan da kwamandan Amurka a Afirka ya yi . Haka kuma Amurka na yunkurin daukar irin matakan da take daukawa Rasha akan Turkiyya. Ana dai ganin baya ga matakan soji da siyasa Amurka na daukar matakan tattalin arziki. Misali, Amurka na bukatar wata bankin Amurka ta rinka kula da shigen fitar kudaden shigar man fetur da ake haka a kasar Libiya. Tana yunkurin wata kanfanin Amurka ta rinka bayar da kididdigar man fetur din kasar Libiya domin babban bankin Amurka. Haka kuma tana bukatar kanfani mai suna Jones ya kula da shigowar kayayyakin tsaro a kasar. Ana dai ganin ya zama wajibi ga Amurka ta yi hadaka da Turkiyya domin cimma burinta a kasar ta Libiya.
Ana dai ganin cewa Amurka da Jamus sun inganta matakan siyasarsu a kasar Libiya fiye da sauran ķasashe. Jakadan Jamus Oliver Owcza ya ziyarci ministoci da ma'aikatun Libiya. Hakan dai na nuni da dan samun wata matsaya siyasa a kasar Libiya sai dai kuma lamari ne da ya biyo bayan hadakar kasuwanci da cinikayya.
Tattaunawar da Turkiyya da Rasha suka yi nada muhinmancin akan tsarin Libiya. Domin hakan na bukatar kara gwababa siyasar ķasar Libiya da kuma kauda sauran kasashe daga ķasar. A yayinda Turkiyya da Rasha ke shirin wata hadaka ce Jamus da Amurka ke yunkurin gudanar da taron Berlin karo na biyu.
A taron dai masu fada a ji na ta nanata shirin samar da lumana ga kasar ta Libiya, lamarin da ake ganin zai kai ga samar da daidaito a kasar. Akan hakan, taron da Turkiyya da Rasha suke gudanarwa baida wata tasiri akan sanya Libiyan ta kasance akan kafafuwanta. Haka kuma taron zai taba harkokin siyasar ķasar Libiya. Haka kuma taron Berlin karo na biyu ka iya sanya wasu sabbin kasashe yin wata sabuwar hadaka . Sai dai a taron za'a nemi baki su fice daga ķasar. Ana dai ganin cewa hawa da saukar siyasar Libiya zata iya faidantuwa da ire iren wadan nan matakan.
Wannan sharhin Dkt Murat Yesiltas ne daraktan harkokin tsaro a Gidauniyar Nazarin Siyasa, Tattalin Arziki da Hallayar Dan Adam watau SETA dake nan Ankara babban birnin ķasar Turkiyya. Ku huta Lafiya.