Ma'aikatar tsaron kasar Azabaijan ta sanar da cewa an samu rikici a kan iyaka tsakaninta da Armeniya.
A cikin bayanin na ma’aikatar tsaro, an ba da rahoton cewa, sojojin Armeniya suna luguden wuta kan wuraren Azabaijan da ke yankin Kelbacer na kan iyaka.
An bayyana cewa sojojin Azabaijan suma sun mayar da martanin da ya dace kuma rikicin ya ci gaba.
Rikici ya barke a bangare guda da misalin karfe 16:00 agogon kasar a jiya, wani soja daga sojojin Azabaijan ya mutu ta hanyar harbi da bindiga daga sansanonin Armeniya.