Rikicin Azerbaijan da Armeniya

Rikicin Azerbaijan da Armeniya

Armenia ta sake nuna fitinarta a Nagorno-Karabakh bayan Tovuz. Ta kara kaimin harin da ta fara kaiwa sojojin Azerbaijan a ranar Lahadi. A wannan rikicin da yawan kauyukan da ta mamaye sun koma hannun Baku. Yerevan da alama ta na cikin lissafi mai tattare da kura kurai. Ankara da dukkanin karfinta ta kasance mai goyawa Azerbaijan baya. Akan hakan ne, bayan harin da aka kaiwa yankin Tovuz, mai nisan kilomita 100 daga Nagorno-Karabakh, a ranar 12 ga watan Yuli, ya sanya Baku sake shiryawa tsaf. Atasayen hadaka da Azerbaijan ta yi da Turkiyya  ya sake nuna irin kwarjinin rundunar sojan Turkiyya. Ba dai za'a iya bayyana cewa rikicin Armenia da Azerbaijan zai koma wani yakin da zai dauki tsawon lokaci ba. Musanman yadda kungiyar NATO, Majalisar Dinkin Duniya da kuma kungiyar OSCE ta Minsk dukkaninsu sun yi kira ga ķasashen da su tsagaita wuta su koma teburin sulhun.

 

Akan wannan maudu'in mun kasance tare da Dkt Murat Yesiltas daraktan harkokin tsaro a Gidauniyar Nazarin Siyasa, Tattalin Arziki da Hallayar Dan Adam watau SETA…

 

A yan kwanakin dake tafe dai ana ganin cewa kungiyar Minsk zata matsa lamba ga bangarorin biyu su koma teburin sulhu. Rashin samar da jituwa da kungiyar Minsk ba ta yi bane ya haifar da harin da Armenia ta fara kaiwa.A shekarar 1991 ne dai Armenia ta mamaye kashi 20 cikin darin kasar Azerbaijan wanda Majalisar Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ta nemi su fice daga yankunan hudu lamarin da Yerevan taki mutuntawa. Duk da dai yarjejeniyar Bishkek na ranar 4-5 ga watan Mayun 1994 ya haifar da tsagaita wuta, kasancewar Nagorno- Karabakh da wasu yankuna 7 Azerbaijan karkashin mamayar Armenia ba abu ne wanda za'a taba amincewa dashi ba. Hakan ne dai ya tabbatar da cewa a Kudancin Caucasian koda yaushe rikici na iya barkewa. Wannan rikicin na  bayyana cewa ķasashen Rasha, Turkiyya da Faransa zasu kasance masu kalubalantar juna da zasu  taka rawar gani.

Akwai dai rikitar da kai ganin yadda rikici ya fara raguwa a yankin Bahar Rum inda Turkiyya da Girka suka fara shirin komawa teburin sulhu ne, fitina da rikici suka barke a yankin Nagorno Karabakh. Abu na farko da yake zuwa zuciya shi ne yadda Rasha ta so rike Yerevan, wacce ke nuna alamun kusantar Amurka, Rashar ta kange hakan  ta hanyar rura wutar rikicin Armeniya da Azerbaijan. Za'a iya tabbatar da hakan kasancewar yadda Yerevan ta juya zuwa Moscow domin neman taimako nan take. Abin tambaya anan shi ne: Ko menene dalilin da ya sanya Rasha wacce ba ta taba janyewa daga ganin Caucasian a matsayin barayinta ba karfafa Yerevan?

Tada kayar baya da kara hura wutar rikicin Armenia da Azerbaijan bayan na Idlib a Siriya da kuma Libiya, ko lamari ne daya kara haifar da gwagwarmayan kalubalantar juna tsakanin Ankara da Moscow? Ko Ankara tana kara kaimin yada sojojinta ne? Ko kuma tana kara neman wani shiri ne game da maslahar Libiya da Siriya? Idan aka ce za'a bayar da amsar wadannan tambayoyin a halin yanzu an yi gaggawa. Hakika kasancewar yadda Amurka ke fuskanta zabe ba za ta iya yin wata katabus akan lamurkan dake faruwa a yankin ba.

Moscow dai  ta sake nuna cewa zata iya karɓar iko ta hanyar haifar da kara hura wutar rikice-rikice a yankin. Ko kuma ķasashen Nahiyar Turai da suka kasance marasa katabus da suka hada da Jojiya, Yukiren da Belarus zasu yi hadakar rufe guraben da Rasha ta bari ne? Zamu dai sanya ido muga tasirin da rokon da Armenia ke yiwa Amurka wacce ke shirin gudanar da zaben shugaban ķasa zai haifar. Abinda ya tabbata anan shi ne irin gurbin da aka bari a tsarin siyasa tun daga Libiya zuwa Gabashin Bahar Rum, Siriya zuwa Caucasian. Haka kuma bayan bulluwar Covid-19 duniya ta sake fadawa cikin yanayin rudani da gwagwarmayan mallakar iko kamar yadda ta kasance bayan yakin duniya na farko. Dan janyewar da Amurka ta yi daga wasu yankunan ya baiwa Rasha damar rufe wasu guraben da ta bari cikin sauki.

 Ķasashen yamman dake kalubalantar kusantar Turkiyya da Rasha, ya kamata su lura da irin daidaiton Rasha a ķasashen Libiya, Siriya da Caucasian. Fafutukar mallakar yanki da ake ta faman yi a doron kasa bai kamata a dubeshi akan yunkurin mallakar yanki ba; kamata ya yi a kallashi a matsayin yunkurin kare muradun ķasa.

 

Wannan sharhin Dkt Murat Yesiltas ne  daraktan harkokin tsaro a Gidauniyar Nazarin Siyasa, Tattalin Arziki da Hallayar Dan Adam watau SETA dake nan Ankara babban birnin ķasar Turkiyya…..


News Source:   ()