Mutane 19 sun samu raunuka a rikicin da ya afku tsakanin sojoji da mutanen da ke zanga-zangar nuna adawa da tabarbarewar yanayin rayuwa a Labanan.
A cikin labaran da kamfanin dillacin labaran kasar NNA ya rawaito, an bayyana cewa mutanen sun dauki matakin toshe hanya ne domin nuna rashin amincewa da tabarbarewar yanayin rayuwa, rashin man fetur da man dizal da kuma magunguna a yankin Cebel Muhsin (Dutsen Muhsin) na birnin Tarabulus.
An bayyana cewa sojoji sun bude wuta a sama kuma 4 daga cikin masu zanga-zangar sun samu raunuka a rikicin da ya afku yayinda rundunonin sojoji suka yi kokarin bude hanyar da masu zanga-zangar suka toshe.
Labarin ya kunshi bayanan cewa an tura sojoji zuwa yankin saboda karuwar tashin hankali.
A cikin wata rubutacciyar sanarwa daga rundunar sojoji ta Labanan, an bayyana cewa sojoji 5 sun samu raunuka sakamakon bam din da aka yi da hannu da matasa suka jefa a yankin Cebel Muhsin kuma wasu sojoji 10 sun samu raunuka sakamakon duwatsun da masu zanga-zangar suka jefa.