Rikice rikicen duniya sun bunkasa kamfanonin kera makamai- Rahoto

Rikice rikicen duniya sun bunkasa kamfanonin kera makamai- Rahoto

Wata cibiya mai zaman kanta dake bincike kan lamurran da tsaro da cinikin makamai a duniya mai hedikwata a birnin Stockholm ce ta wallafa rahoton, wanda ya ce a shekarar 2023 kaɗai, cinikin makamai da sauran kayayyakin soji da kamfanoni 100 mafiya girma a fannin suka yi, ya kai na dalar Amurka biliyan 632, kwatankwacin ƙarin kashi 4.2 cikin 100 idan aka kwatanta da baya.

Ƙididdiga ta nuna cewar a shekarar 2022 kamfanonin ƙera makaman 100 dake Rasha da yankin Gabas ta Tsakiya sun fuskanci ƙarancin kuɗaɗen shiga saboda gazawar da suka tasanma yi wajen biya buƙatun abokan cinikinsu, sai dai akasarin kamfanonin sun samu nasarar ƙara yawan makaman da suke ƙerawan a shekarar bara ta 2023.

Wasu daga cikin alƙaluman da rahoton ya fitar sun haɗa da ƙaruwar cinikin makaman wasu manyan kamfanonin Rasha biyu da kashi 40 cikin 100, yayin da takwarorinsu da dama a Gabas ta Tsakiya suka samu karin cinikin da kashi 18 cikin 100, sakamakon yakin Rasha a Ukraine da kuma rikcin Gaza, sai kuma wasu kamfanonin kera makamai na Japan da hada-hadarsu ta ƙaru da kashi 35 cikin 100.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)