Rikice-rikice na dakile yaki da Korona a doron kasa

Rikice-rikice na dakile yaki da Korona a doron kasa

Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta sanar da cewa duk da kiraye-kirayen da ake yi na dakatar da rikice-rikice yayin sabon nau'in cutar coronavirus (Kovid-19), rikice-rikice sun ci gaba a sassa daban-daban na duniya, wanda hakan ya sanya kokarin yaki da annobar ke kara wuya.

Jami'an Majalisar Dinkin Duniya a taron kwamittin tsaron MDD da aka yi ta yanar gizo sun yi nazari kan halin da fararen hula ke ciki a yankunan da ake ci gaba  da tafka rikici. 

Mataimakin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya kan Harkokin Jin Kai Mark Lowcock ya yayin yaki da Covid-19, rikice-rikice a yankuna daga Syria zuwa Yemen, daga Jamhuriyar Demokradiyyar Congo zuwa Mozambique sun ci gaba, kuma wannan ya yi mummunan tasiri ga kokarin kula da mutanen da suka kamu da cutar.

Lowcock ya ce, dakatar da zirga-zirgar jiragen sama, rufe iyakoki, takaita tafiye-tafiye da kuma matakan kebewa na hana isar da kayan agaji zuwa yankunan da ake rikici.

"A lokaci guda kuma, cin hanci da rashawa, takunkumi, matakan yaki da ta'addanci da shingayen gudanarwar gwamnati sun sanya gudanar da ayyukan jin kai wuya."


News Source:   ()