Republican ta kama hanyar samun rinjaye a zauren majalisun Amurka

Republican ta kama hanyar samun rinjaye a zauren majalisun Amurka

Duk da cewa hankula sun fi karkata kan wanda zai yi nasarar jagoranta White House a shekaru 4 masu zuwa tsakanin Donald Trump na Republican da Kamala Harris ta Democrat, a gefe guda kowanne guda cikin waɗannan ƴan takara biyu na fatan ganin jam’iyyarsa ta samu rinjaye a zauren majalisun don samun sauƙin aiwatar da manufofinsa ba tare da cin karo da tarnaƙi ba.

Daga yammacin Virginia gwamnan jihar mai ci Jim Justice na jam’iyyar Republican ne ya lashe kujerar bayan kayar da Joe Manchin na Democrats, yayinda can a Ohio Republican ɗin ta lashe ta hannun ɗan takararta Bernie Moreno wanda ya kayar da Sherrod Brown na Democrats.

Zaurukan majalisun Amurka 2 da ke ginin Capitol na ƙunshe da ƴan majalisu ne 435 waɗanda dukkaninsu aka kaɗa ƙuri’ar zaɓensu sai kuma Sanatoci da ke da kujeru 100.

Alƙaluman da ake tattarawa ya nuna yadda Republican ke samun tagomashi a dukkanin majalisun biyu bayan da kujerar Justice da Moreno suka kufcewa Democrts inda yanzu ƙirgen ke shirin sauya daga 51 da 49 tsakanin manyan jam’iyyun biyu zuwa wani yanayi daban, musamman idan har Republican ɗin ta lashe kujerun Montana da Wisconsin da kuma Pennsylvania.

Alamu na nuna yiwuwar Democrats ta yi kankankan da Republican a jihohin Texas da Florida.

Idan har Republican ta lashe dukkanin kujerun da alamu ke nuna za ta yi nasara akansu kenan za ta iya tashi da kujerun majalisar dattijan 55 cikin 100 wanda zai basu damar mara baya ga manufofin Trump idan ya yi nasara haka zalika tarnaƙi ga manufofin Kamala Harris idan ita ta yi nasara.

A karon farko mata baƙa fata 2 sun samu kujerun majalisar dattijan bayan nasarar Angela Alsobrooks da Lisa Blunt Rochester na Democrats a Maryland da Delaware.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)