Republican na shirin kunna wa Biden wuta kan ficewar Afghanistan

Republican na shirin kunna wa Biden wuta kan ficewar Afghanistan

Rahoton wanda ɗan Majalisa Michael McCaul ya jagoranci haɗa shi ya zargi mahukuntan Amurka ƙarƙashin shugaba Joe Biden da jinkirta aikin kwashe dakarun ƙasar daga Afghanistan baya ga rashin mutunta tsarin kwashe fararen hular ƙabul da suka cancanci guduwa saboda fargabar mayaƙan Taliban.

Rahoton ya ce sai a ƙurataccen lokaci ne gwamnatin Biden ta bayar da umarnin fara kwashe fararen hula Amurkawa da sauran jami’ai waɗanda ba yaƙi suka shiga Afghanistan yi ba, umarnin da aka bayar ranar 16 ga waatan Agusta lamarin da ya sanya aikin kwashe Amurkawan cikin yamutsi.

Michael McCaul wanda shi ne shugaban kwamitin kula da harkokin wajen Amurka na jam’iyyar Republican, ya ce sun shafe shekaru 3 suna gudanar da bincike kan wannan babban laifi na gwamnatin Biden da ya kai ga sakacin barin tarin fararen hula a cikin haɗari.

McCaul ya bayyana cewa, matakin Joe Biden ya nuna yadda Amurka ta nuna halin ko’in kula ga ƙawayenta.

Shi kansa tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya yi kakkausar suka ga Biden da Harris waɗanda kai tsaye ya ɗora alhakin mace-macen da aka samu yayin yamutsun na filin jirgin saman Abbey Gate da ke Ƙabul akansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)